sudanesehausa
الإخوة والأخوات الزوار ندعوكم للتسجيل ونرحب بمشاركتكم وتعليقاتكم

sudanesehausa

منتدى قبيلة الهوسا Discussion Board
 
الرئيسيةس .و .جبحـثدخولالتسجيل

شاطر | 
 

 marubutan hausa

اذهب الى الأسفل 
كاتب الموضوعرسالة
dansudan

avatar

ذكر
عدد الرسائل : 221
مكان الإقامة : من ابناء ودرعية [ الجزيرة ] مقيم في هولندا
تاريخ التسجيل : 08/07/2007

مُساهمةموضوع: marubutan hausa   السبت أغسطس 04, 2007 6:47 pm

ABDUL'AZIZ AHMAD ABDUL'AZIZ
abdulazizfagge@ yahoo.com
mylittlewisdom@ maktoob.com
08037763251
064945529
“Harshen Hausa ya gawurta
Harshen Hausa ya yalwanta
Harsshen Hausa fifita
Harshen Hausa ya inganta
Sosai ya dararwa waninsa”
--Marigayi Mal. Aqilu Aliyu
Farfesa Joseph McIntyre, asalinsa baturen kasar Aiylan ( Ireland ) ne, amma an haife shi ne a qasar Ingila. Sunansa na Hausa kamar yadda mafi yawan turawa masu sha'war harshen hausa suke da shi, shi ne Malam Gambo. Shi ma kamar sauran 'yan uwansa farar fata masu bincike akan harshen Hausa, ya bada gudunmmawa mai yawa domin bunqasar wannan harshe na hausa.
Kodayake dai shi McIntyre asalinsa malami ne a fagen koyar da halayyar xan adam wato "Sociology" amma ko da zuwansa Kano a cikin shekarar 1974 sai kawai ya koma ka'in da na'in vangaren bincike a cikin harshen Hausa. Amma, kamar yadda bahaushe yake cewa "Da walakin, goro a miya", Malam Gambo a lokacin karatunsa na digiri na biyu, ya karanta al'adun 'yan Afrika ne tare da xaukar kwas a Hausa, saboda haka nema daga bisani ya komo ga harshen Hausan gaba xaya.
A lokacin da ya zo kano a cikin shekarar 1974, Farfesa McIntyre ya zauna a gidan Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya dake unguwar Gwammaja har tsawon shekara xaya daga bisani kuma sai ya koma unguwar Kurmawa duk dai a cikin birnin Kano . Mal. Gambo ya koyar a jami'ar Bayero dake Kano daga shekarar 1975-1980. A shekarar 1980 ya samu aiki a jami'ar Hamburg dake qasar Jamus domin koyar da Hausa.
Na samu takardun gayyata daban-daban zuwa wurin taron da cibiyar nazarin al'adun hausawa ta shirya tare da haxin gwiwar gamayyar qungiyoyin marubuta na jihar Kano , inda aka shirya Farfesa Joseph McIntyre (Mal. Gambo) zai kasance babban baqo mai jawabi. Na samu waxannan takardun gayyata ta hanyar majalisun yanar giza-gizan sadarwa ta intanet da nake ciki, wato majalisar marubuta da majalisar masoya da writers forum Kano da ANA-Kano.
Ranar da aka shirya gudanar da taron kamar yadda sanarwar ta bayyana ita ce ranar Alhamis ashirin da takwas ga watan yuni na shekarar dubu biyuda bakwai, (2007). An kuma shirya gudanar da taron ne a xakin karatu na Murtala Muhammed dake birnin Kano , za kuma a fara ne da misalin qarfe huxu na yamma. Sakamakon sha'awa da nake da ita kan adabi da zamantakewar Hausawa da kuma cigaban harshen Hausa don haka tun da na ga waxancan takardun gayyata sai na kudiri aniyar halartar wannan taro, sakamakon sha'awa da nake da ita kan adabi da zamantakewar Hausawa da kuma cigaban harshen Hausa.
Kodayake ba wannan ne karo na farko da na tava saduwa da wani bature mai sha'awar harshe da kuma al'ummar Hausawa ba, amma wannan ne karo na farko da zan halarci wani taro da wani bature zai yi magana akan harshen Hausa.
A baya na tava saduwa da fararen fata da suka bada gudunmawa ga cigaban harshen Hausa ko kuma tarihi da al'adun Hausawa, kamar irinsu Farfesa Graham Furniss da Farfesa Murray Last da Carmen McCaine (Talatu) da kuma shugaban sashen Hausa na rediyon Jamus, Malam Mosh, amma dukkaninsu ban tava risqar lokacin da suka gabatar da wata muqala ko jawabi cikin, ko akan harshen Hausa ba. Wannan ya qara samin sha'awar in halarci wannan taro na ranar 28 ga watan yuni musamman da yake ban tava gamuwa da shi Farfesa McIntrye ba, uma ban tava halartar taron da wani bature ya ga gabatar da jawabi (muqala) cikin Hausa ba.
Amma cikin ikon Allah a wannan rana ta Alhamis yayin da nake jiran lokacin da aka ajiye domin gabatar da shirin (qarfe hudu na yamma) ya cika, sai kwatsam ruwa ya kece. To fa! Nan dai nayi ta fatan janyewar ruwan kafin qarfe huxun nan ta cika. Cikin ikon Allah kuwa, 'yan mintun kafin lokacin sai aka xauke ruwan, to sai fa shirin tafiya.
Na yi dace ba a fara gudanar da taron ba a lokacin da na isa wu rin, amma ba da jimawa ba aka fara. Bayan buxe taro da addu'a sai shugaban taron Farfesa Abdu Yahaya Bichi ya yi taqaitaccen jawabi daga nan kuma sai ya umarci Farfesa Sa'idu Ahmad Vavura da ya gabatar da babban baqo, wanda aka taru dominsa wato Farfesa McIntyre (Mal. Gambo).
Farfesa Vavura ya yi cikakken bayani dangane da ko wanene Farfesa McIntyre (Malam Gambo), tare da bayyana irin gudunmawar da yake bayarwa wurin bunqasa harshen hausa. Farfesa Vavur, ya yi misali da wani sabon littafi da shi Mal. Gambo ya wallafa mai suna "Hausa Verbal Compound", wanda Farfesa Vavura ya ce bai tava ganin zuzzurfan aiki a wannan vangare na nahawun Hausa kamar shi wannan littafi ba.
A cewar Farfesa Vavura, Mal. Gambo mutum ne da a koyaushe yake barin qofarsa a buxe ga Hausawa mazauna qasar Jamus ko kuma waxanda wani uzuri ya kaisu can xin. Bayan kammala jawabin gabartarwar sai mai gayya mai aiki wato Farfesa McIntyre ya karvi ragamar jawabin.
Babban abin da ya burge mutane shi ne yadda wannan bature ya shafe tsawon lokaci yana zuba magana cikin Hausa kamar jakin Kano . Daxin daxawa tare da yin amfani da balagar zance da hikimomin magana.
Tunda fari Mal. Gambo ya bayyana ma'anar wannan suna na shi (McIntyre) wnda ya ce gamayya ne na yaren qasar Aiylan da faransanci wanda gaba xaya dai ke nufin "Xan qasa". Don haka nema ya ce shi xan qasa ne a duk inda ya je musamman qasar Hausa.
Haka zalika, lokacin da Farfesa Abdulqadir Xangambo ya tambaye shi ko ya aka yi ya samu sunan Mal. Gambo, ganin cewa McIntyre da Mal. Gambo ba su da amsa amo ko ma'ana iri xaya? Sai Farfesa McIntyre ya ba shi amsa da cewa "Kafin in zo Kano ban san me ake nufi da Gambo ba, ballantana Xan Gambo". Bayan an dara sakamakon wannan barkwanci, sai Mal. Gambo ya bayyana cewa wanda ya laqaba masa wannan suna shi ne Malam Aminu Mani, wani tsohon ma'aikacin sashen Hausa na gidan radiyon BBC wanda suka yi sabo da shi tun a London .
Ya ce a lokacin da ya zo Kano a cikin 1974 sai ya ziyarci Mal. Aminu Mani, shi kuwa nan take ya shawarci McIntyre cewa tun da har ya zo qasar Hausa ( Kano ), to lallai ya kamata a sa masa sunan Hausawa. Bayan McIntyre ya ba shi taqaitaccen tarihinsa cewa shi an haife shi ne bayan an haifi tagwaye a gidansu, sai kawai Mal. Mani ya ce to ai wannan ya dace da Gambo a Hausa, daga nan ne Farfesa Joe McIntyre ya samu sunan Malam Gambo.
Mal. Gambo ya kuma bayyana cewa, asalinsa ba baturen Ingila ba ne, amma sakamakon hijira da kakanninsa suka yi zuwa Ingila daga ainihin qasarsu ta Aiylan ( Ireland ), sai aka haife shi a arewacin Ingila. Saboda haka nema ya ce "Ni xan ci-rani ne". Ya kuma bayyana cewa wannan hijira ta afku ne sakamakon talauci a qasar Aiylan wanda mulkin mallakar Ingila ya haifar a qasar.
Da ya juya kan maudu'in taron kuwa,wato "Hausawa a uwa duniya". Farfesa McIntyre, ya yi cikakken bayani dangane da halin da Hausawa dake zaune a garin Hamburg na qasar Jamus ke ciki. Ya yi bayani irin halin quncin da suke ciki sakamakon rashin cikakkiyar fahimtar juna da take tsakaninsu da jama'ar garin.
Kodayake, ya bayyana cewa bai tava ganin cikakken Bahaushe xan Najeriya ba a cikin irin waxancan masu zaman quntatar. Ya ce Hausawa da suke zaune a Hamburg dukkaninsu ba su shige su xari ba kuam sun fito ne daga qasar Ghana sai kuma 'yan qabilar Ashanti waxanda sune 'yan Afrika da suka fi yawa a garin.
Sai dai waxancan 'yan Afrika dake zaman halin ha'ula'i a Hamburg su na shiga qasar Jamus ne ba tare da izini ba sai kawai su fake da neman mafakar siyasa wanda kuma baya bisa qa'ida. Kuma yawanci suna yin qananan ayyuka ne a kamfanoni inda ake biyansu abinda bai taka kara ya karya ba. Dan haka ne ma Farfesa McIntyre, ya ce ya sha shawartar irin waxancan mutane a kan su dawo gida ganin irin wahalar da suke sha.
Mal. Gambo dai ya share tsawon lokaci yana jawabi ba tare da gajiyawa ba har ma sai da aka tsaida shi sakamakon gabatowar duhun magariba domin a samu damar yin tambayoyi da kuma sharhi.
Na fuskanci, kamar yadda nima na gamsu kusan dukkanin waxanda suka halarci wannan taron sun yi matuqar gamsuwa tare da samun annashuwa daga yadda sshi babban baqon ya gabatar da jawabinsa. Daga qarshe Farfesa Abdallah Uba Adamu ya yi jawabin godiya sannan kuma aka rufe taron da
الرجوع الى أعلى الصفحة اذهب الى الأسفل
http://hausa-language.blogspot.com/
 
marubutan hausa
الرجوع الى أعلى الصفحة 
صفحة 1 من اصل 1

صلاحيات هذا المنتدى:لاتستطيع الرد على المواضيع في هذا المنتدى
sudanesehausa :: الفئة الأولى :: المنتدى الأول :: Hausa :: Magana-
انتقل الى: