Harshen Afrika na farko a kan babban rediyon duniya
Rfi rediyo na farko a kasashen Afrika renon Faransa, ya kara fadada shirye shiryensa ga masu saurare, tare da bunkasa manufofinsa a nahiyar.
Daga ranar litanin 21 ga watan Mayu shekara ta 2007 kai tsaye daga dakin shirya labarunsa da ked a cibiya a Muryar Nijeriya Lagos, Rfi zai watsa shirye shiryensa a cikin harshen Hausa na tsawon awa biyu 2 a kowace rana.
A kowace safiya akwai shirye-shirye guda biyu:
Daga karfe 6 TU zuwa 6 30 TU, wato Karfe 7 zuwa 7 30 agogon Nijeriya, Nijar, Kamaru da Cadi.
Da kuma karfe 7 TU zuwa 7 30 TU, wato karfe 8 zuwa 8 30 agogon Nijeriya, Nijar, Kamaru da Cadi.
Tare da shirin awa daya kulun da yamma, da misalin karfe 4 zuwa 5 TU wato karfe 5 zuwa 6 agogon Nijeriya, Nijar Kamaru da Cadi.
Nahiyar Afrika dai, na kumshe da kimanin al'umma Milyan 80 da ke magana a cikin harshen Hausa, wadanda Rfi ke da burin gabatar masu da shirye-shiryensa, tare da nuna kwarewarsa wajen bada labaran da su ka shafi duniya da kuma nahiyar Afrika.
A Nijar za a iya kama mu ne kan mita 96.2 zangon FM a biranen: Niamey - Maradi - Zinder - Tahoua.
A sauran sassan duniya kuma za a iya kama mu a kan mita 19 da 41 gajeren zango.
Lanni Smith - Project Co-ordinator (234 (0) 8068792439)
Atayi Ezéchiel Opaluwah - Press contact (234(0) 8055109320)
E-mail:
hausa.rfi@gmail.com